Kokarin ceto bankin Credit Suisse a Switzerland
March 16, 2023Talla
Durkushewar bankin da ba a taba samun makamanciyarta ba a Switzerland ta haifar da shakku a fadin kasar tare da saka abokan huldar bankin na Creditn Suisse cikin damuwa.
Tuni dai gwamnatin Switzerland ta umurci babban bankin kasar ta ya ya ranta zunzutun kudi biliyan 50 na kudin kasar wa bankin na Credit Suisse don kubutar da shi daga wannan matsalar tare kuma da kiran masu hannun jari da su ci gaba da mu'amala da bankin.
Gwamnatin Switzerland ta sanar da mahinmancin daukar matakan gaggawa don ceto bankin wanda ke zama na biyu mafi girma a kasar