Yunkurin ceto darajar Euro
February 4, 2011Shugabannin kasashen Tarayyar Turai masu fada aji suna ganawa a birnin Brussel, inda batun ceto faduwar darajar takardar euro ya kasance gaba a jadawalin taron. Duk da cewa taron na yau an tsara shi ne don tattauna batun makamashi, ya kuma duba kudurin da kasashen Jamus da Faransa suka gabatar, kan tsuke bakin aljihun gwamnatocin kasashen dake amfani da kudin euro, a wani mataki na tsamo su daga dimbin bashin da suka fada. A wani jawabin hadin gwiwa da suka yi wa manema labarai, shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da shugaban kasar Farasa Nicolas Sarkozy, sun bayyan cewa za su yi aiki tare da shugaban hukumar Tarayyar Turai Herman Van Rompuy don yanke shawara nan da karshen watan gobe, ko za su cimma wata matsaya kan matakin bai daya na ceto takardar kudin euro.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Abdullahi Tanko Bala