Yunkurin dakatar da yakin Gaza
January 8, 2024Kasar Amirka da kawayenta na wani sabon yunkurin hadin wgiwar ganin an dakatar yakin sojoji a Gaza. Wani labarin da ya fito daga mahukuntan kasar Italiya ya bayyana cewa yanzu kawancen kasashen na iya kokarinsa don ganin an shawo kan Isra'ila da ta dakartar da bude wuta. A bisa wannan yunkurin yanzu haka sakataren harkokin wajen Amirka Anthony Blinken da ministar harkokin wajen Jamus Annalena Baerbock da babban jami'in harkokin waje na Tarayyar Turai Josep Borrell, duk suna ziyartar yankin a wannan makon don kokarin yayyafa ruwa kan rikicin na Isras'ila da Palasdinawa, wanda yanzu haka ke karar fadada a yankin Gabas ta Tsakiya. A bangaren ziyararsa sakataren harkokin wajen Amirka Anthony Blinken ya fara ne da kasar Jordan da Katar, kafin ya wuce Saudiyya da Isra'ila an ji shi yana magana da kakkausar muryar neman Isra'ila ta kare fararen hula, ita kuwa ministar harkokin wajen Jamus Annalena Baerbock ta kasance ne a cikin kasar Isra'ila, inda ta yi kira da Isra'ilan ta son cewa babban alhakinta ne don kare fararen hulan Falasdinawa a Yammacin kogin Jordan. Yayaninda Josep Borrell ya sauka Lebanon, wanda duk cikin kokarin yayyafa ruwa ne ga rikicin na Israila da Palasdinawa wanda aka fara tun bayan harin da Hamas ta kai a ranar bakwai ga watan Oktobar bara.