Matsin lamba kan 'yan ta'adda tsakanin Faransa da G5 Sahel
July 1, 2020Talla
A yayin wani taron kolinsu da suka kammala a yammacin jiya a birnin Nouakchott na Murtaniya, shugaba Emmaneul Macron ya ce sojan kasashen hadin gwiwa da takaransu na Faransa, sun fatattaki masu tayar da kayar bayan a wasu iyakokin Mali da Nijar da Burkina Faso, inda masu da'awar jihadin suka fi tsananta kai hare-hare a baya bayan nan tare da kwace sansanoninsu da dama, yana mai cewa wannan mataki zai ci gaba dorewa kana kuma za a kara adadin jam'an tsaro a makonin dake tafe domin rundunar hadin gwiwar kasashen da na Turai mai suna Takuba ta mamaye wuraren da aka karba a hannun 'yan ta'adda.