Yunkurin daidaita farashin makashi a Turai
September 30, 2022Talla
Ana sa ran a taron ministocin su tsayar da farashin iskar gas da wutar lantarki da kamfanoni ke samarwa, bayan da ya yi karanci a nahiyar tun soma yakin Ukraine.
Kana taron ministocin zai kuma tantance bukatar rage amfani da makamashin da akalla kaso 5% a lokuttan aiki a daukacin kasashen nahiyar Turai, sannan kuma akwai batun zartar da matakin farko da hukumar EU ta gabatar na tallafin kudade ga masu amfani da makamashi don rage masu radadi.
Jamus kasa mafi karfin tattalin arziki a nahiyar Turai, ta bayyana anniyarta ta samar da kudi Euro biliyan dari biyu don daidaita tsadar farashin makashi a kasar.