1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabon

Fafutukar warware rikicin siyasar Gabon

Zainab Mohammed Abubakar
September 5, 2023

Sabon jagoran mulkin sojin Gabon ya gana da mai shiga tsakani na tsakiyar Afirka, bayan juyin mulkin da aka yi a makon da ya gabata wanda ya kawo karshen mulkin sai Mahadi ka-ture na shekaru 55 na daular Bongo.

https://p.dw.com/p/4VzRT
Janar Brice Oligui NguemaHoto: AFP/Getty Images

Gidan talabijin kasar Gabon ya ce Janar Brice Oligui Nguema ya gana da shugaban kasar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya Faustin Archange Touadera bayan juyin mulkin da aka yi ranar 30 ga watan Agusta. Kungiyar raya Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Tsakiya (ECCAS) ta nada Touadera a matsayin mai shiga tsakani wajen ganin an sake maido da kasar ta Gabon tafarkin dimukradiyya. A kan haka ne aka dora masa alhakin ganawa da dukkan bangarorin da abun ya shafa da nufin samar da hanyar sake komawa ga tsarin mulki cikin sauri. 

GabonGabon mai arzikin man fetur ta hade da sauran kasashen Afirka da kamar Mali da Guinea da Sudan da Burkina Faso da Nijar, da suka fuskanci juyin mulki a cikin shekaru uku da suka wuce, al'amarin da ya haifar da fargaba a nahiyar da ma sauran kasashen.