1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Limaman Coci sun yi addu'o'i ga 'yan gudun hijira

Salissou Boukari
July 7, 2018

Manyan jagororin adinin Kirista na kasashen Siriya da Lebanon sun ziyarci birnin Bari da ke Kudancin Italiya, tare da yin kira ga kasashen duniya da su taimaka wajen mayar da 'yan gudun hijiran Siriya gidajensu.

https://p.dw.com/p/30zOy
Papst Franziskus in Bari
Hoto: picture-alliance/AP Photo/A. Tarantino

Manyan jagororin na Coci sun yi amfani da wata dama ce ta ganawa da za su yi a wannan Asabar din da Fafaroma Franscis, wanda zai gana da kusan dukannin manyan limaman Coci-Coci na yankin Gabas ta Tsakiya a wannan birni mai babbar tashar ruwa, domin nuna goyon bayansu ga kiristoci na yankin Gabas ta Tsakiya.

Ba da dadewa ba ma Jagoran 'yan darikar katolika na duniya Fafaroma Franscis, ya sanar cewa, da suna ci gaba da yin salloli na roko kan halin da 'yan uwansu maza da mata ke ciki na tashin hankali sakamakon rikice-rikice.

Jagororin adinin na Kirista na yankin Gabas ta Tsakiya ta bakin babban jagora Kirista na kasar Lebanon, sun yi kira ga kasashen Yamma da  da su bada kwarin gwiwa ga 'yan gudun hijiran Siriya na ganin sun koma ya zuwa gidajensu.