Yunkurin ministan Pakistan na kare Islama
September 23, 2012Ministan sufuri na kasar Pakistan ya yi alkawarin bayar da ladan dubu 100 na dollar Amirka, ga duk wanda ya kashe mutumin da ya shirya fim din batanci ga addinin musulunci a Amirka. Jaridar "Dawn" da ake bugawa kulli yaumin a Pakinstan ta ruwaito cewa Ghulam Ahmad Bilour ya nemi hadin kan 'yan taliban da kuma al-Qaida a yunkurin da ya ke yi na kare Islama.
Sai dai wani kakakin firaministan kasar ya ce minista Bilour ya yi gaban kansa ne, saboda ba gwamnati ba ta da ruwa wajen daukan wannan mataki. Mutane da daman gaske ne dai suka rasa rayukansu a kasar ta Pakistan yayin da wasu suka jikata a cikin wannan makon da muke ciki, a lokacin zanga-zangar yin Allah wadai da faifain na batanci. Ana kyautata zaton cewar shi mutumin da ya shirya wannan fim, wani kirista ne da ke bin mazhabar koptik da ke kyamar musulmi.
Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Umaru Aliyu