Kokarin shigar da agajin gaggawa a Siriya
February 13, 2023Talla
Shugaban hukumar agajin gaggawa ta Majalisar Dinkin Duniya Martin Griffiths da ya kai ziyara a karshen makon jiya a kasashen Turkiyya da Siriya, zai gabatar da cikakken rahoton halin da ake ciki game da bukatar kai kayan agaji a kasashen biyu.
Tun da farko ma dai sai da shugaban hukumar ya bayyana kasawar kasashen duniya game da shigar kayyakin agaji musamman a yankin arewa maso yammacin Siriya, kazalika shugaban ya bayyana cewar da akwai bukatar bude hanyoyin shigar da kayayakin agaji ga mabukata a cikin hanzari.
Ya zuwa yanzu dai iftila'in girgizar kasa a kasashen Turkiyya da Siriya ya halaka akalla mutane fiye da dubu 35, baya ga wasu dubban jama'ar da suka jikkata.