1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bangarorin da ke rikici a Burundi na shirin yin sulhu

Lateefa Mustapha Ja'afarJuly 18, 2015

A wani mataki na karshe domin shawo kan rikicin siyasar kasar Burundi gabanin zaben shugaban kasa, bangaren gwamnati da na 'yan adawa sun bude sabon babin tattaunawa.

https://p.dw.com/p/1G115
Zanga-zamgar siyasa a Burundi
Zanga-zamgar siyasa a BurundiHoto: Getty Images/AFP/C. de Souza

Rikicin siyasar ta Burundi dai da ake fargabar kada ya juye zuwa yakin basasa ya samo asali ne sakamakon kafewa da shugaban kasar mai ci yanzu Pierre Nkurunziza ya yi kan cewa sai ya sake tsayawa takarar shugabancin kasar a karo na uku, abin kuma da ya sabawa tanade-tanaden kundin tsarin mulkin kasar.

A ranar Talata 21 ga wannan wata na Yuli da muke ciki ne dai ake sa ran gudanar da zaben shugaban kasa a Burundin, zaben kuma da 'yan adawa suka dage kan cewa za su kaurace sakamakon abin da suka kira da yin tazarce karo na uku na Shugaba Nkurunziza ya saba yarjejeniyar sulhun da ta kawo karshen yakin basasar kasar da aka cimma a shekara ta 2006.

Tun cikin watan Afirilun da ya gabata ne rikicin siyasa ya barke a kasar ta Burundi sakamakon bayyana kudirin yin tazarce a karo na uku da Shugaba Nkurunziza ya yi.