Yunkurin warware rikicin gabashin Ukraine
June 26, 2014Mai magana da yawun shugabar ta gwamnatin Jamus din ne ya tabbatar da wannan bukata da ta mikawa Mr. Putin, wadda ita ce irinta ta biyu a wannan makon, kuma ya ce Merkel din ta yi hakan ne don ganin an tsawaita batun tsagaita wutar da gwamnatin Ukraine ta amince da ita a baya wadda ke karewa cikin daren yau.
Shi ma dai sakataren harkokin wajen Amirka John Kerry irin matsayi daya ya dauka da shugabar ta gwamnatin Jamus, inda dazu a birnin Paris na Faransa ya ke cewar ya kyautu Rasha ta nuna cewar da gaske ta ke game da kawo karshen halin da gabashin Ukraine din ke ciki.
Gabannin wannan dai, 'yan awaren Ukraine din da ke dasawa da Rasha sun sanar da cewar sun amince da a yi wata tattaunawa ta kawo karshen rikicin a gobe Juma'a a birnin Donesk, batun da kasashen da ke kokarin shiga tsakani a rikicin suka yi na'am da shi.
Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Usman Shehu Usman