Yunkurin warware takaddamar nukiliyar Iran
June 8, 2012Hukumar makamashin nukiliya ta duniya za ta zauna kan teburin tattaunawa a wannan juma'ar a birnin Vienna da hukumomin Iran, da nufin neman bakin zaren warware matsalar shirin makamashin kasar da ake takaddama a kai. Babban burin da kwararru na IAEA suka sa a gaba shi ne cimma yaryejeniya da za ta ba su damar ziyartar cibiyoyi makamashin Iran domin tantance ko kasar na shirin kera makamin kare dangi koko a'a.
Shugaban hukumar makamashin nukiliya ta duniya wato Yukiya Amano ya wallafa wasu bayani da ke nuna cewar Iran ta yi yunkurin mallakar makamin nukiliya. Sai dai fadar mulki ta Teheran ta yi watsi da wannan zargi, ta na mai cewa shirinta na makamashi na zaman lafiya ne. IAEA na neman Iran ta bata izinin yi wa cibiyar nukiliya ta Parchin tsinke domin duba zahirin abin da ke faruwa.
Wannan taron ya zo ne kwanaki goma kafin ganawa da manyan kasashen duniya da Jamus da ita kanta Iran za su yi game da shirin nukiliyar da ake cece kuce a kai. sakatariyar harkokin wajen Amirka Hilary clinton ta nemi Iran ta bayar da hadin kai, yayin da kasashen Turai suka nemeta ta dakatar da shirin inganta Uranium da ta sa a gaba.
Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Abdullahi Tanko Bala