1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yunwa na kara muni a kasashen Afirka

June 28, 2022

Miliyoyin mazauna da dama daga cikin kasashen Afirka na fama da karancin abinci sakamakon matsalolin fari da na rikice-rikicen 'yan bindiga da ke karuwa a yanzu.

https://p.dw.com/p/4DMrh
Südsudan Kandak 2018 | Frau & Sorghumhirsen nach Essensabwurf WFP
Hoto: Sam Mednick/AP Photo/picture-alliance

Matsalar karancin abinci da ke addabar gabashin Afirka, na ci gaba da muni a Sudan ta Kudu inda miliyoyin mutane ke cikin mawuyacin hali.

Kimanin mutum miliyan bakwai da dubu 700 ne ke fama da matsanancin karancin abincin a Sudan ta Kudu, adadin kuma da ya haura rabin al'umar kasar.

Kungiyoyin agaji da kan taika wajen sama wa wasu daga cikin 'yan kasar tallafin abincin, na kokawa da matsalar karancin kudade, abin kuma da ya tilasta su rage taimakon da suke bayarwa.

Sama da mutum miliyan 60 da ke yankuna da dama na gabashi da ma yammacin Afirka a yanzu ke bukatar taimakon abinci, saboda matsaloli na fari da ma rikice-rikice da suke fama da su.