UNICEF: Yunwa na kashe yara a Sudan
August 14, 2024Shugabar Asusun Kula da Ilimin Kananan yara na Majalaisar Dinkin Duniya UNICEF Catherine M. Russell ce dai, ta nuna wannan takaici kan yadda karancin abinci a Sudan ta kai ga zama silar mutuwar daruruwan yara kanana a makon da ya gabata. Shugabar ta UNICEF ta kara da bayyana cewa, Sudan ita ce kasa mafi yawan yaran da suka rasa matsugunansu a duniya wasu miliyoyi kuma ke fuskantar karancin abinci mai gina jiki da kuma rashin zuwa makaranta. Russell ta bayyana cewa akwai kimanin yara miliyan tara a Sudan da ba sa samun isasshen abinci yadda ya kamata, inda miliyan hudu daga cikinsu ke fuskantar karancin abinci mai gina jiki.
Shirin Samar da Abinci na Majalisar Dinkin Duniya ya nunar da cewa, barnar da yunwa za ta yi a Sudan ka iya dara wacce yakin basasar da aka kwashe shekara guda ana yi muddin ba a gaggauta shigar da kayn agaji kasar ba. Wata mata da yunwa ta kashe 'yarta a yankin Kordofan a kudancin kasar ta Sudan, ta ce tana fata duniya ba za ta bar yunwar ta gama da sauran 'ya'yanta uku da suka rage wadanda suma a yanzu suke fama da yunwar ba. Majalisar Dinkin Duniyar dai, ta yi kira ga bangarorin da ke gwabza yaki su gagauta bayar da damar shigar da kayan agaji. Tun a farkon wannan watan na Agusta wasu kwararru a fannin kula da abinci suka yi hasashen cewa, zuwa watan Satumbar da ke tafe kaso 70 cikin 100 na al'ummar Sudan za su iya fuskantar matsananciyar yunwa.