1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yunƙurin ceto Girka daga ramin basuka

July 21, 2011

An buɗe taron ƙasashen da ke amfani da kuɗin euro domin laluɓo han'yar tsamo ƙasar Girka daga rikicin tattalin arziki da ta faɗa

https://p.dw.com/p/120uO
Ministocin kuɗi daga ƙasashen dake amfani da EuroHoto: AP

Ƙasar Faransa da Jamus sun ɗauki matsiyi guda kan rikicin basuka na ƙasar Girka, gabanin taron gaggawa na ƙasashen da ke amfani da kuɗin euro da aka fara gudanarwa yau a birnin Brussels. Kakakin shugabar gwamnatin Jamus bai yi ƙarin haske kan matsayin da ƙasashen biyu suka ɗauka ba, amma yace an cimma matsayar bayan ganawa da aka yi daren jiya a birnin Berlin, tsakanin shugaba Sarkozy na Faransa da Angele Merkel shugara gwamnatin Jamus. Ƙasar Girka dai na buƙatan ƙarin tallafin kuɗi, kimanin euro biliyan 110, domin ta samu tafiyarda harkan kuɗin ta nan da shekaru uku a gaba. Hukumar Tarayyar Turai ta yi gargaɗin cewa tattalin arzikin duniya zai ji a jika, muddin dai ba a samu matsaya ba a taron na yau. Yan kasuwa na gudun cewa idan Girka ta karye, to hakan zai shafi ɗaukacin ƙasashen da ke amfani da kuɗin euro, ciki harda wadanda ke da ƙarfin tattalin arziki.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Umaru Aliyu