1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yunƙurin Jamus na shiga tsakani a rikicin Izra'ila da Falasɗinu

February 25, 2014

Jamus ta gargaɗi Izra'ila da cewar ci gaba da gina sabbin matsugunai a yankunan Falasɗinawa na janyo cikas ga ƙoƙarin warware rikici a yankin.

https://p.dw.com/p/1BEo5
Angela Merkel und Benjamin Netanjahu
Hoto: Reuters

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, tare da tawagarta ta wasu ministocinta na ci gaba da ziyarar yini biyu a Izra'ila domin tattaunwa da mahukuntan ƙasar. Tun gabannin ziyarar ce kuma, Merkel ta sake yin kira ga buƙatar yin aiki tare, domin samar da ƙasashen biyu na Izra'ila da Falasɗinu, waɗanda zasu zauna daura da juna cikin zaman lafiya da lumana.

A wannan Litinin (25. 02.14) kuma, ministan harkokin wajen Jamus Frank-Walter Steinmeier ya yi suka ga manufar Izra'ila ta ci gaba da gina sabbin matsugunan Yahudawa a yankunan Falasɗinawa da ke gabar tekun Jordan: Ya ce "Tun a can baya ne muka fito fili muka bayyana cewar, faɗaɗa matsugunai a yankunan Falasɗinawa ba ya taimaka wa ƙoƙarin warware rikicin da ke ci gaba da wanzuwa a tsakanin sassan biyu, kuma zamu sake bayyana wa mahukuntan Izra'ila wannan matsayin."

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Abdourahamane Hassane