1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tallafi ga ƙasashen da ke fama da bakin haure

Kamaluddeen Sani /LMJAugust 10, 2015

Hukumar Ƙungiyar Tarayyar Turai ta amince da bayar da tallafin kuɗaɗe har kimanin Euro miliyan 4,200 don taimaka wa wasu ƙasashen ƙungiyar da suka haɗa da Girka da Italiya.

https://p.dw.com/p/1GCtv
Bakin haure da ke kwarara nahiyar Turai
Bakin haure da ke kwarara nahiyar TuraiHoto: picture-alliance/dpa/Z. Gergely Kelemen

Ƙasar Italiya za ta karɓi kusan Euro miliyan 5,60 yayin da Girka za ta karɓi Euro miliyan 4,73, sakamakon ƙalubalen da suke fuskanta na kwararowar baƙin haure da ke biyowa ta teku. Ɗaruruwan baƙin haure ne dai suka rasa rayukansu daga watan Janairu na wannan shekara kawo yanzu, mafi yawansu daga yankin Gabas ta Tsakiya da kuma nahiyar Afirka a ƙoƙarin da suke na neman mafaka a nahiyar Turai. Kazalika hukumar ta Tarayyar Turai ta ce za ta amince da ƙarin wasu shirye-shirye nan da ƙarshen wannan shekara da za su amfani ƙasashen Turan da kuma 'yan gudun hijirar.