Yunƙurin wasu al'umomi Filato a Najeriya na girka sabuwar jiha
July 13, 2012Samakon yadda jihar Filato ke fama da tashe tashen hankula fiye da shekaru goma ba tare da samun wani cigaba ba, al'ummomin yankin kudanci tare da na tsakiyar Filato, sun yunƙuro don ganin an ƙirƙiro musu da wata sabuwar jiha don su fice daga jihar Filato ta yanzu.
A zancen nan da ake ma dai, batun ƙirƙiro da jihar Filato ta kudu dai tuni har ya iso gaban komittin majalisar ƙasa game da ƙirƙiro da sabbin jihohi a Najeriya, inda wata majiya ta sirri ta tsegunta cewar akwai alamun za'a ƙirƙiro da wasu sabbin jihohi goma, a Najeriya nan gaba.
Sabuwar jihar dai idan an same ta, za ta ƙunshi yankunan jihar Filato ta yanzu 11, daga cikin 17, kuma hakan zai haɗo yankunan tsakiya ne da kudancin Filato, cikin harda Bokkos da Mangu, inda ake sa ran kafa shelkwata a Pankshin, don wannan dalili nema tuni har fittatun mutane 'yan hasalin yankin irin su Alh. Yakubu Useni, Farfessa John Wade da wasun su, suka himmatu wajen isar da wannan manufa gaban majalisar ƙasa, to ina aka kwana ne yanzu, Hon. Sadat Garga, ɗan majalisar dokokin Filato ne daga mazaɓar Kantana, kuma yana daga wanda da suka kai wannan ƙudiri na sabuwar jihar Filato ta kudu gaban majalisar tarayya, yayi min karin bayani.
To amma ga dukan alamu, wannan yunƙuri na al'ummar kudanci da na tsakiyar Filato yanzu ba samun jihar su baiyi wa gwamnatin Filato daɗi ba, ko minene ya sa ita gwmnatin ke shure wannan ƙudiri.
Akasarin al'ummar da na zanta da su game da wannan ƙudiri dai sun bayyana min cewar yin hakan babban cigaba ne ga al'umma, to sai dai gwamnatin jihar tana gani ana ƙoƙari ne a ware wata al'umma.
Yanzu haka dai masu wannan yunƙuri sun yi nisa, kenan lokaci ne zai nuna mai zai kasance kan wannan ƙuduri.
Mawallafi: Abdullahi Maidawa
Edita: Yahouza Sadissou Madobi