1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Neman mafita kan bakin haure a Turai

Suleiman Babayo
June 22, 2018

Shugabannin kasashe 16 da ke cikin mambobin kasashen Tarayyar Turai sun nuna yuwuwar samun mafita kan matsalolin bakin haure.

https://p.dw.com/p/306c6
Brüssel Jean-Claude Juncker, Europäische Kommission
Hoto: picture-alliance/AP Photo/O. Matthys

Shugabannin kasashe 16 da ke cikin kungiyar Tarayyar Turai sun nuna yuwuwar samun mafita ta bai daya lokacin taron da za su gudanar a birnin Brussels na Beljiyam ranar Lahadi mai zuwa game da bakun bakin haure masu neman mafata cikin kasashen.

Babban jami'in kungiyar Jean-Claude Juncker ya kira taron saboda duba matsayin kasashen Italiya da Girka wadanda suka karbi galibin bakin haure masu shiga ta gabar teku, domin ganin cewa sauran kasashen na Turai sun shiga an dama da su kan hanyoyin magance matsalolin gami da rarraba bakin haure tsakanin kasashen.

Shugabannin manyan kasashen kungiyar ta Tarayyar Turai da suka hada da Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, da Shugaba Emmanuel Macron na Faransa, da Firaminista Pedro Sanchez na Spain, gami da Firaminista Joseph Muscat na Malta duk bayyana cewa za su halarci taron na Belgium kan hanyar magance matsalolin bakin haure a Turai.