1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaɓe da zanga-zanga a Spain

May 22, 2011

A kasar Spain an fara kaɗa ƙuri'a daura da zanga-zangar da aka shiga tun wasu 'yan kwanaki da suka gabata don nuna adawa da manufar tattalin arziƙi

https://p.dw.com/p/11LH4
Hoto: picture-alliance/dpa

A ƙasar Spain ana gudanar da zaɓen hukumomin birane daura da zanga-zangar da aka shiga domin nuna rashin amincewa da yadda gwamnatin ke tinkarar matsalar taɓarɓarewar tattalin arziƙi. Sama da mutane miliyan 34 suka canacanci kaɗa kuri'a a zaɓen na yau. Ana dai hasahen cewa Fraministan Jose Rodriguez Zapatero na jam'iyyar Socialist zai sha kayi dubi da yadda dubun dubatan jama'a suka yi dafifi a birane 30 a faɗin kasar domin gudanar da zanga-zanga duk kuwa da haramci da gwamnatin ta sanya akan yin hakan. Matsayin rashin aikin yi a ƙasar ta Spain shine irinsa mafi muni tsakanin ƙasashen Ƙungiyar Tarayyar Turai. A dai 'yan shekarun da suka gabata matsayin aikin yi tsakanin matasan ƙasar ya kai kashi 45 daga cikin ɗari. A shekara mai zuwa ne kuma za gudanar da zaɓen gama gari a kasar ta Spain.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Zainab Mohammed Abubakar