Zaɓen Majalisar Dokoki a Girka
June 16, 2012A wannan Lahdin, al'umar ƙasar Girka ke zaɓen 'yan majalisar dokoki.
Wannan zaɓe da zai haƙiƙance makomar ƙasar a sahun ƙasashe masu amfani da takardar kuɗin Euro ya jawo cece-kuce mai tsanani a cikin da wajen Girka.
ƙididigar jin ra' ayin jama' a ta yi hasashen za a kunnen dokoki tsakanin jam'iyar 'yan mazan jiya ta ND, da kuma 'yan gurguzu masu tsatsauran ra'ayin kishin ƙasa.
Shugaban wannan jam' iya Alexis Tsipras ya yi alƙawarin da zaran ya samu rinjaye zai rosa yarjejeniyar da aka cimma tsakanin Girka da ƙasashen EU game da ceto ƙasar daga ƙangin kariyar tattalin arziki.
Sama da kashi uku cikin huɗu na al'umar ƙasar ta Girika na goyon bayan amfani da takardun kuɗin bai ɗaya na Euro, sai dai suna adawa da matakan tsuke bakin aljihu kamar yadda suka a yanzu. Jam'iyun siyasar ƙasar na ƙoƙarin amfani da wannan bambamcin ra'ayin domin taka rawar gani a zaɓen. Bisa al'ada 'yan ra'ayin mazan jiya ma'abota tattalin arziki ne inda suke ɗaukar kansu a matsayin waɗanda za su ba wa ƙasar kyakkyawan matsayi a Turai. Sai dai a lokaci guda suna da niyar sauƙaƙa matakan tsuke bakin aljihun gwamnati.
Su kuwa a nasu ɓangaren 'yan ra'ayin sauyi sun ayyana matakan tsimin kuɗi da cewa haramtacce ne, amma suna son Girika ta ci-gaba da amfani da kuɗin Euro
Mawallafui: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Mohammad Nasiru Awal