Zaɓen shugaban ƙasa a Aljeriya
April 9, 2009Yau ne al´umar ƙasar Algeria ke zaɓen shugaban ƙasa.Bayan kwaskwarimar da aka yiwa kundin tsarin mulki, shugaba mai ci yanzu, Abdel Aziz Bouteflika na daga jerin ´yan takara shidda dake fafatawa a wannan zaɓe.
Bayan sati ukku na yaƙin neman zaɓe a yau al´umar Aljeria ta fito, domin ta kaɗa ƙuri´a, wadda a sakamakon ta za a tantance mutumen da zai ɗauki ragamar shugabacin ƙasa daga jerin ´yan takara shida, wanda suka haɗa da shugaba Abdel Aziz Bouteflika, dake kan karagar mulki, tun shekara ta 1999.
Shugaban ya alƙawarta samar da zaman lafiya a Aljeria bayan fama da tayi cikin yaƙin basasa, wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane kusan dubu ɗari biyu.Magoya bayansa sun yi imanin cewar, Aljeriya sai shi, ta la´akari da yadda ya cimma nasara shinfiɗa kwanciyar hankali da kuma bunƙasa tattalin arzikin ƙasa kamar yadda ɗaya daga masu goyan bayan nasa ya bayyana:A yanzu kwanciyar hankali ta samu ko ina mutum zai iya zama waje har zuwa karfe uku karfe hudu na dare, ba tare da zullumi ba.Amma kafin hawan Bouteflika kan karagar mulki, tun baki ƙarfe shidda, indan an je nesa ƙarfe bakwai na yamma, babu kowa cikin titina, yanzu kau sai mutum ya kwana waje idan yana buƙata.
To saidai kamar yadda hausawan kance, ra´ayi riga ce , a tunanin Kader Abderrahim wani ɗan Aljeria dake hukumar husa´a da bincike a game da ma´amilar ƙasa da ƙasa ta birinin Paris na ƙasar France,mulkin Adel Aziz Bouteflika,mulki ne irin na kama karya:
talakawan basu ji daɗin wannan mulki Majalisar Dokoki na matsayin ´yar amshin shata, sannan kotuna basu da cikkaken ´yanci, sai kuma kafofin sadarwa wanda ke cikin takunkumi da ƙuntatawa, mulki ne kawai, irin na hamdama da babakere.
A lokacin yaƙin neman zaɓe, dukkan´yan takara guda shidda, sun gabatar da manufofinsu da burrurukansu ga al´umar ƙasa, to saidai duk da haka, dama daga Aljeriyawa na nuna halayen ko in kula.
Ni dai a ra´ayina, ɓaɓatu maras fa´ida, cemma jawabai ne wanda muka saba ji.
Tunni dai masu kulla da harakokin siyasar a ƙasar Algeria un yi imani da cewa idan ba wata ƙaddara ba, shugaba Abdel Aziz Bouteflika za shi tazarce, domin tuni mafi yawa daga jam´iyun adawa sunyi kira ga magoya bayansu su ƙauracewa zaɓen, sannan sauran ´yan takara biyar da fafatawa basu da ƙarfin gwagwarmaya tare da shi.
Babu wani mai shakku a game da nasara shugaba Bouteflika, saidai ayar tambaya itace, ƙaƙa zai fuskanci alƙawuran da yayiwa jama´a bayan ya sake ɗarewa kan karagar mulki.
Algeria dai ƙasa ce mai arzikin gaske, ta la´akari da ɗimbin albarkatun man fetur da ta mallaka, gwamnati tayi amfani da wani sashe na wannan kuɗaɗe a cikin gine ginen hanyoyi da gidaje, to saidai jama´ar ƙasar na fama da talauci,matasa na fama da rashin aikin yi saboda haka da dama daga cikinsu ke kwarara zuwa ƙasashenTurai, wanda kuma suka tsaya gida suka ruggumi ƙaddara, na ɗauke da fatan ganin ƙasar ta karɓi taken da ake mata, na "lu´ulun tsakiyar ruwa".
Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi.
Edita: Umaru Aliyu