1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaɓen yan majalisun dokoki a ƙasar Girka

September 16, 2007
https://p.dw.com/p/BuBE

A Girka, an kammala kaɗa ƙuri´ar zaɓen yan majalisun dokoki, da aka gudanar yau a faɗin ƙasar baki ɗaya.

Rahottani daga Athenne, babban birnin ƙasar, sun ruwaito cewar, ƙiddidigar bayan fage, ta ba Praministan Costas Caramanlis rinjaye, saɓanin yadda a ka zata.

Da dama daga masu kulla da harakokin siyasa, sun nunar da cewa, Praministan zai faɗi a wannan zaɓe, ta la´akari da sukar da ya ke sha, daga al´ummar ƙasa, a sakamakon kasawar da ya nuna, wajen kawo ƙarshen gobara da ta lalume yankuna masu yawa a watan da ya gabata.

A cewar bayyanai daga kafofin sadarwa na ƙasar Girka, ya zuwa yanzu jam´ iyar ND, ta Praminista na da kimanin kashi 43 cikin ɗari, na ƙuri´un da aka jefa, a yayin da jam´iyar yan gurguzu mai adawa, ta tashi da kashi kussan 39 cikin ɗari.

Nan gaba a yau, ake sa ran bayyana sakamakon zaɓen baki ɗaya, saidai ayar tambaya har yanzu itace ko Costas zai samu gagaramin rinjaye kokuma a´a.