1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaArewacin Amurka

Za a ba da tallafin corona a Amirka

Ramatu Garba Baba
December 22, 2020

'Yan majalisar wakilan Amirka sun amince da wani kuduri na tallafin ceto kasar daga annobar corona. Kudurin dai ya sami kuri'ar amincewar 'yan majalisa akalla 91 a yayin da bakwai kacal suka nuna rashin goyon baya.

https://p.dw.com/p/3n2B3
USA Washington | Coronavirus | Trump und Mitch McConnell
Hoto: Erin Schaff/Pool/Getty Images

Tallafin zai lakume kimanin dala biliyan 900. A daren jiya Litinin aka cimma wannan matsaya bayan da aka dade ana kai ruwa rana a bukatun samar da kudadden tallafi na murmurewa daga radadin corona. Ana sa ran shugaban kasar Donald Trump zai sanya hannun nan da 'yan kwanaki masu zuwa kafin a soma aiwatar da aikin.

Za a yi amfani da wadannan kudadden wajen taimaka wa kamfanoni da masana'antu da kuma wadanda suka rasa aiyukansu. Amirka ce a sahun gaba daga cikin kasashen duniya da ta tafka asarar rayuka da dukiya a sanadiyar corona, mutum sama da miliyan goma sha takwas cutar ta kama wasu fiye da dubu dari uku suka mutu. 

A daya bangaren zababben Shugaban kasar Joe Biden ya karbi allurar rigakafin cutar inda ya kara tabbatar ma 'yan kasa cewa babu wani abin fargaba a game da rigakafin.