1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ukraine za ta karbi jiragen yaki

Abdoulaye Mamane Amadou
August 27, 2022

Birtaniya za ta ba wa Ukraine tallafin jiragen ruwa maras matuka da ka iya lalubo muggan nakiyoyin da Rasha ta binne a gabar teku, in ji ma'aikatar tsaron kasar.

https://p.dw.com/p/4G8lM
Ukraine Soldat Drohne FlyEye WB Electronics
Hoto: Efrem Lukatsky/AP Photo/picture alliance

A cikin wata sanrwar da ta fitar, ma'aikatar tsaron ta Birtaniya ta ce jiragen na iya nuta mai cin dogon zango har mita 100 a kasa, kana kuma ana iya amfani da su a wuraren da ke sa sassaucin zurfi na ruwan teku a cikin hanzari.

Ko baya ga kyautar jiragen guda shida, Birtaniya ta kuma sha alwashin horar da jami'an sojin Ukraine yadda za su amfani da sabbin makamai a wani mataki na kare kansu daga mamayar Rasha.

Ana dai zargin ko akwai yiwuwar Rasha ta binne manyan nakiyoyi a karkashin tekun Ukraine don hadasa tarnaki wa gabar ruwa Bahar Aswad da Ukraine ke amfani da ita wajen fitar da kayayakin abinci da take nomawa zuwa kasuwannin duniya.