1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hosni Mubarak ya daukaka kara a kotun EU

Abdourahamane Hassane
December 12, 2018

Wata kotun kungiyar tarrayar Turai ta yi watsi da karan da tsohon shugaban kasar Masar Hosni Mubarak ya daukaka na rike wasu kudadensa da ake ci gaba da yi a cikin bankuna cikin wasu kasashe na EU.

https://p.dw.com/p/39wdj
Ägypten Ex-Präsident Mubarak Militärkrankenhaus
Hoto: Reuters/M. Abd El

 Kotun ta kungiyar EU da ke a Luxemburg ta  kori  karan sannan ta kara tsawaita ci gaba da rike kudaden na tsohon shugaban kasar Masar din a cikin bankuna. Hosni Mubarak mai shekaru 90 da haifuwa a shekara ta 2011 wata kotun a Masar  ta wankeshi a game da zargin  da ake yi masa na kisan masu zanga-zanga, sai dai kuma an ci gaba da tsareshi a gidan kurkuku a kan laifin cin hanci, tun a shekara ta 2011 bayan juyin juya halin da ya shareshi daga mulki.