1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Za a fara rarraba maganin rigakafin Maleriya

December 8, 2022

Bayan kwashe shekaru ana fadi tashin ganin an samo rigakafin cutar Maleriya, a karshe Majalisar Dinkin duniya ta sanar da shirin fara samar da alluran ga miliyoyin yara.

https://p.dw.com/p/4KgmE
Hoto: dpa/picture alliance

Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya WHO, ta ce an kammala shirye-shirye na fara amfani da sabuwar allurar rigakafin cutar zazzabin cizon sauro wato Maleriya, aikin da ake sa ran ya ceto rayukan miliyoyin kananan yara wadanda ke mutuwa galibi a kasashe matalauta.

Sama da kasashe 20 ne a cewar WHO za su samu magungunan rigakafin na Maleriya samfurin RTSS, kasashen kuma da cutar ta fi gallaza wa yara a cikin su a cewar Abdisalan Noor babban jami'in da ke kula da shirin yaki da cutar.

Kimanin mutane dubu 619 ne Maleriyar ta kashe a shakarar da ta gabata a duniya, yayin da a shekarar 2020 adadin wadanda suka mutu da ita suka kai dubu 625.

Adadin wadanda ke kamuwa da cutar ya kai mutum miliyan 247 kuma kashi 95% suna kasashe ne na Afirka.