1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ghana ta samu tallafin rigakafi

February 24, 2021

Ghana ta zama kasa ta farko da ta fara karbar tallafin Majalisar Dinkin Duniya na rigakafin Corona

https://p.dw.com/p/3pp4o
Ghana | AstraZeneca | COVAX-Impfstoff
Hoto: Francis Kororoko/REUTERS

A karkashin tsarin nan na Majalisar Dinkin Duniya na tallafin alluran rigakafin Corona wato COVAX, Ghana ta zama kasa ta farko da ta fara karbar tallafin a fadin duniya.

Kimanin alluran na kamfanin harhada magunguna na AstraZeneca 600,000 ne kasar ta karba a wannan laraba.

Babban daraktan hukumar lafiya ta duniya Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce hakan na zama wani babban cigaba da aka samu na yaki da annobar kuma ba za a kawo karshen ta ba har sai an game ko ina da rigakafin.

Ghana kamar sauran kasashen duniya da suka fara bayar da rigakafin, za a fara ne da mutane mafiya hadarin kamuwa da cutar kamar tsofaffi da masu rashin lafiya ta musamman da kuma ma'aikatan kiwon lafiya.