Za a je zagaye na biyu a zaben kasar Iran
June 30, 2024Daga cikin kuri'u miliyan 24 da rabi da aka kada, dan takara mai sassaucin ra'ayi Masoud Pezeshkian, wanda kwararren likitan zuciya ne, ya samu kuri'u miliyan 10 da dubu 400.
Mai biye masa kuwa shi ne Saeed Jalili wanda ke da kuri'u miliyan tara da dubu 400 a cewar ma'aikatar kula da al'amuran cikin gida.
Kakakin majalisar dokokin kasar ta Iran wanda shi ma ke takarar, ya samu kuri'u miliyan uku ne da dubu 300, sai kuma Malamin Shi'ar nan Mostafa Mohammad Bagher Qalibaf, ke da kuri'u dubu 200 da doriya.
Babu dai dan takara guda daga cikin hudun da ya samu sama da kaso 50% na ilahirin kuri'un a Iran da zai ba shi nasara a dokance.
Karkashin dokar zaben kasra ta Iran dai za a je zagaye na biyu a tsakanin 'yan takara biyu ne da suka fi yawan kuri'u, kuma tuni aka bayyan ranar Juma'a biyar ga watan Yulin da ke shirin kamawa a matsayin ranar zagayen na biyu.