1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Za a je zagaye na biyu a zaben Laberiya

October 25, 2023

Ta tabbata za a je zagaye na biyu a zaben shugaban kasa da aka yi a Laberiya, bayan rashin rinjaye mai karfi a tsakanin Shugaba George da babban abokin takarasa Joseph Boakai.

https://p.dw.com/p/4Xzxi
Madugun hamayya Joseph Boakai da Shugaba George Weah
Madugun hamayya Joseph Boakai da Shugaba George Weah Hoto: picture alliance/dpa/epa/Reynolds/Jallanzo

Shugaban kasar Laberiya George Weah na kan gaba a zagayen farko na zaben kasar da aka yi.

To sai dai kuma shugaban na Laberiya bai samu kuri'un da za su ba shi galaba kai tsaye a zaben ba, ganin kankantar rata da ke tsakaninsa da madugun adawa Joseph Boakai.

Hakan dai na nufin za a je zagaye na biyu ke nan a zaben da ke zama fafatawa irinta ta farko a tsaknin manyan masu takarar a zaben na Laberiya.

A shekara ta 2017 ne dai Shugaba George Weah wanda tsohon zakaran kwallo ne, ya yi nasara a kan Joseph Boakai da sama da kashi 60% na kuri'u.

Shi dai madugun adawa Boakai shi ne ya yi wa tshohuwar shugabar kasar wato Ellen Johnson Sirleaf mataimaki a baya.