Gaza: Ana dakon zuwan kayan agaji da magunguna
January 17, 2024Isra'ila da ke yaki da kungiyar Hamas ta Falasdinu, ta sake jefa bama-bamai a zirin Gaza, inda za a aike da magunguna ga mutanen Isra'ila da aka yi garkuwa da su a matsayin bani gishiri na baka manda na taimakon agaji ga al'ummar Falasdinu, a wani bangare na yarjejeniyar da Faransa da Qatar suka cimma. Shaidu sun yi magana musamman game da tashin bama-bamai a kusa da asibitin Nasser inda a cewar sojojin Isra'ila, shugabannin Hamas da Isra'ila da Amurka da tarayyar Turai suka ayyana a matsayin kungiyar 'yan ta'adda ke buya.
Isar da magunguna ga wadanda aka yi garkuwa a Gaza
Qatar ta ba da sanarwar wata yarjejeniya kan shigar da magunguna ga wadanda aka yi garkuwa da su a madadin jigilar kayan agaji ga fararen hula a zirin Gaza. Za a aika da magunguna da taimakon a ranar Laraba zuwa Al-Arich, a Masar, a cikin jiragen sama biyu na sojojin Qatar, tare da ra'ayin canja wurin su zuwa zirin Gaza in ji shugaban diflomasiyyar Qatar a ranar Talata. Yanzu haka mutane 250 da aka yi garkuwa da su zuwa Gaza , inda aka sako kusan 100 daga cikinsu yayin da aka yi sulhu a karshen watan Nuwamba na jiran samun taimakon magunguna. A cewar hukumomin Isra'ila, 132 na ci gaba da zama a yankin Falasdinawa, inda 27 daga cikinsu ake kyautata zaton sun mutu.