1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Za a kara yawan dakaru a yankin Sahel

July 17, 2021

Babban sakataren  majalisar Dinkin Duniya  Antonio Guterres ya bukaci kwamitin tsaro na majalisar da ya fadada ayyukan tsaro a yankin yammacin Afirka musamman a yankunan Sahel.

https://p.dw.com/p/3wd2C
Frankreich Mali - Militär Konflikte
Hoto: Frederic Petry/Hans Lucas/picture alliance

Bukatar hakan ta biyo bayan wani harin da aka kai wa dakarun wanzar da zaman lafiya na majalisar, makwanni uku da suka gabata a lardin Gao da ke arewa maso gabacin Mali, wanda ya yi sanadiya hallaka sojojin gwamnati goma sha biyu wasu goma sha uku suka ji mummunan rauni da suka hada da sojojin Jamus goma sha biyu da na Baljiyan guda daya rak.

Kimanin karin dakarun wanzar da zaman lafiyar 2,069 ne, ake sa ran aike wa a yankin da suka hada da dakarun soji 1,730 da na 'yan sanda dari uku da wani abu.