Za a kashe mutane 75 a Masar
July 28, 2018Talla
Wata kotu a kasar Masar ta yanke wa wasu mutane 75 hukuncin kisa, ciki har da shugabannin kungiyar nan ta 'yan uwa Mususlmi ta Muslim Brotherhood da magoya bayansu.
Su dai mutanen an zarge su ne da gudanar da zanga-zanga da kuma zaman dirshen a shekara ta 2013, inda suka goyi bayan hambararren Shugaban Masar din Mohammad Morsi.
Wannan dai wani hukunci ne na wucin-gadi da mutum 739 ke fuskantar fushin doka.
Bayan hukuncin na yau Asabar, za kuma a mika batun ga babban Mufti na kasa don yanke hukuncin karshe, kamar yadda yake a tsarin dokokin Masar.
A ranar 8 ga watan Satumba ne kuma za a yanke wa wasu mutum 660 hukunci.