1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Za a koma teburin neman tsagaita wuta a Gaza

July 8, 2024

Ana sa ran sake komawa zaman tattaunawa a kan kokarin tsagaita wuta a Zirin Gaza a wannan makon, kamar yadda rahotanni na baya-bayan nan a kan yakin ke nunawa.

https://p.dw.com/p/4i1Cu
Wasu daga cikin jagorori masu duba rikicin Gaza a birnin Doha
Wasu daga cikin jagorori masu duba rikicin Gaza a birnin DohaHoto: HAMAS MEDIA OFFICE/REUTERS

Jami'ai da dama da ke nazari a kan yakin watanni tara da Isra'ila ta kaddamar a kan Zirin Gaza, na ganin girman asarar da aka tafka na iya sanya kungiyar Hamas ta sassauta wasu bukatunta ta yadda za a kai ga cimma matsaya.

Ko a karshen mako ma dai kungiyar ta Hamas ta jingine guda daga cikin manyan bukatunta na cewa sai Isra'ila ta dakatar da yakin kafin ta amince da tattaunawa a kan tsagaita bude wa juna wutar.

Ofishin Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu, ya sanar da cewa wakilan kasar za su koma teburin tattaunawar birnin Doha na kasar Qatar.