1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Za a sake bude makarantu a China

Abdourahamane Hassane
May 26, 2022

A Kasar China za a sake bude makarantun kwaleji da sakandri a birnin Shanghai a watan Yuni da ke tafe a wata alama ta sassauta dokar kule da aka saka a birnin saboda sake barkewar cutar corona.

https://p.dw.com/p/4Bu1r
Schule in Schanghai
Hoto: AP

Sakamakon sake bullar annobar a china hukumomin sun tilasta wa jama'a zaman gida tun a cikin watan Afrilun da ya gabata musammun ma a birnin na Shanghai cibiyar tattalin arzikin kasar mai yawan al''umma miliyan 25. Gwamnatin ta China ta ce an fara samun saukin cutar don haka, an dage haramci da dama da aka yi na takaita walwalar jama'a.