1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Za a sake tattaunawa kan rikicin Siriya

Ahmed Salisu
July 10, 2017

Wakilan gwamnatin Syria da na 'yan tawayen kasar za su sake yin wani zama a wannan Litinin din domin tattaunawa da nufin shawo kan rikicin kasar wanda aka shafe kimanin shekaru 6 ana gudanar da shi.

https://p.dw.com/p/2gFH9
Kasachstan Syrien Friedensgespräche in Astana Opposition
Hoto: Reuters/M. Kholdorbekov

Zaman wanda Majalisar Dinkin Duniya ke jagoranta zai gudana ne a birnin Geneva na kasar Switzerland kuma za a tattauna ne kan samawa kasar sabon kudin tsarin mulki da zaben da kuma hanyoyin da za a bi wajen kawo karshen masu aikata aiyyuka irin na ta'addanci a kasar.

Manzon musamman na Majalisar Dinkin Duniya kan rikicin na Siriya Stefan de Mistura ya ce duk da cewar an dau lokaci ana irin wannan zama, amma ya zuwa yanzu akwai wagegen gibi tsakanin bangarorin da ke kokarin warware banbance-banbancen da ke tsakaninsu.

Sau tari dai 'yan adawar Siriya kan gabatar da bukatarsu ta ganin Shugaba Assad ya sauka daga mulki sai dai wakilan gwamnatin kasar da kan halarci irin wannan zaman kan nace cewar batun makomar Assad din ba abu ne da za su yadda a tattauna a kai ba.