Za a samar da rigakafin Corona ta farko a Afirka
May 30, 2021Talla
A wata ziyarar aiki da su ka kai a kasar Afirka ta Kudu, ministan lafiya na Jamus Jens Spahn da shugaba Emmanuel Macron na Faransa sun yi alkawalin tallafa wa Afirka ta Kudu wajen samar da rigakafin COVID-19 ta farko a Afirka.
Spahn ya bayyana cewa Jamus din za ta saka hannun jari na kimanin yuro miliyan hamsin a ayyukan samar da rigakafin, tare da kuma taya Afirka ta Kudun zawarcin kamfanonin harhada magunguna na yammacin duniya domin misayar kimiyya da fasahar harhada rigakafin.
Afirka ta Kudu na cigaba da fadi tashin ganin ta yi wa al'ummarta milayan 60 rigakafin ta Corona, inda kawo yanzu kaso biyu cikin dari ne na yan kasar aka sami nasarar yi wa allurar zagaye na farko.