1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jami'an Rasha da UKraine za su tattauna

Abdullahi Tanko Bala
February 28, 2022

A wannan Litinin ake sa ran tattaunawa tsakanin Jami'an Ukraine da na Rasha a iyakar Belarus. Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky ya amince da tattaunawar yayin da sojojin Putin ke kara kutsawa cikin kasarsa 

https://p.dw.com/p/47hbW
Symbolbild Treffen | Putin Zelenskyy
Hoto: Russia/Ukraine Press Offices/AP/picture alliance

Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky ya amince da tattaunawar yayin da sojojin Putin da tankokin yaki suke kara kutsawa cikin kasarsa 

A waje guda Shugaban Rasha Vladimir Putin ya umarci sojojinsa masu kula da makamin nukiliya su kasance cikin shirin ko ta kwana.

Vladimir Putin ya kara kambama tashin hankali tsakanin yankin gabashi da yammaci bayan da ya umarci sojoji masu kula da makamin nukiliya su zauna cikin shiri.

Putin ya danganta matakin da abin da ya kira kakkausar sanarwar da NATO ta yi da kuma tsauraran takunkumin tattalin arziki da aka sanyawa kasarsa.

Wannan dai ya sanya fargabar cewa rikicin na Ukraine na iya rikidewa zuwa yaki da makamin kare dangi walau da ganga ko kuma da kuskure.

Amirka ta bukaci Putin ya sassauta kausasan kalamai masu hadari da yake yi na barazana da makamin Nukiliya.