1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Muna shirin tura masu bincike a Izyum

Abdoulaye Mamane Amadou
September 16, 2022

Majalisar Dinkin Duniya na duba yiwuwar aika tawagar bincike a Izyum bayan zargin da Ukraine ta yi na yi wa fararen hula sama da 400 kisan gilla tare da rufe su a kabari daya.

https://p.dw.com/p/4GzRh
Ukraine-Krieg - Isjum - Massengrab
Hoto: Evgeniy Maloletka/AP/dpa/picture alliance

Ofishin kare hakin bani Adama na Majalisar Dinkin Duniya ya ce wakilansa da ke sa ido kan batun kare hakin dan Adam a Ukraine na bibiyar batun, kuma nan da gaba za su kai ziyara a yankin Kharkiv da dakarun Ukraine suka kwace a baya bayan nan daga hannun Rasha.

Shugaba Volodymyr Zelensky ya zargi Rasha da aikata kisan gilla ga fararen hula a Izyum, tare da bayyana cewa ya zama wajibi a saka haske kan kabarin da aka sama da gawarwaki.

Shugaba Zelensky ya ce akwai bukatar duniya ta bude idonta don ganin irin ta'asar da Rasha ke yi a ci gaba da mamayar da take yi a Ukraine.