1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Shugaban Ghana zai fara karbar rigakafin COVID-19

March 1, 2021

Shugaban Ghana Nana Akufo-Addo ya yi kira ga 'yan kasar da su yi watsi da masu nuna shakku a game da sahihancin allurar rigakafin cutar coronavirus gabanin kaddamar da fara shirin rigakafin cutar a wannan Talata.

https://p.dw.com/p/3q2ou
Ghana Präsident Nana Addo Dankwa Akufo-Addo
Hoto: Anthony Anex/KEYSTONE/picture alliance

A Jawabi ga 'yan kasar, Nana Akufo-Addo ya ce ba gaskiya bane a ce wai idan mutum ya yi rigakafin corona, kwayar halittarsa za ta sukukuce ko kuma wai za ta hana magidanta haihuwa, yana mai musanta wadanda ke cewa Turawa sun kawo rigakafin coronavirus domin karar da mutanen Afirka.

Shugaban na Ghana ya ce domin ya tabbatarwa 'yan kasar gaskiyar abin da yake fadi, shi da kansa da mai dakinsa da mataimakinsa da kuma matar mataimakinsa za a fara yi wa rigakafin a wannan Litinin kuma a bainar jama'a. 

Ghana ce dai kasa ta farko a Afirka da ta samau tallafin rigakafin corona ta AstraZeneca guda 600,000 daga Majalisar Dinkin Duniya karkashin tsarin nan na COVAX a makon da ya gabata, kuma tana fatar fadakarwa za ta sanya 'yan kasar su saki jikinsu su karbi rigakafin ta corona da hannu biyu.