Za ka iya zaga Jamus da tikitin Euro tara
A watannin Yuni da Yuli da kuma Agusta, za a samu tikitin jirgin kasa a kan Euro tara kacal a fadin Jamus. Matakin na zuwa ne domin ragewa al'umma radadin tsadar makamashi a sakamakon yakin Rasha da Ukraine.
Gadar Ravenna da ke Black Forest
Zai iya zaman tafiya cikin jirgin kasa a Jamus mafi birgerwa a tarihi: A watannin Yuni da Yuli da kuma Agusta na 2022, kudin tikiti na tafiye-tafiye da dama a jirgin kasa zai kasance Euro tara kacal. Tikitin zai kasance na tafiye-tafiye a dukkan ababen hawa, wato motocin bas-bas da jiragen kasa. Kar ku manta da Black Forest da kuma ketara gadar Ravenna a kudancin Jamus.
Gabar Kogin Rhine
A jirgin ruwa ko mota, tafiya a Kogin Rhine za ta zamo abin tarihi matuka. Guda daga cikin wurare abin birgewa, shi ne gabar Kogin Rhine. Gabar ruwan ta hada garuruwan Bingen da Rüdesheim da kuma Koblenz. Akwai tsofaffin gidajen tarihi da kauyuka abin birgewa. Hukumar Kula da Ilimi da Wuraren Tarihi ta Majalisar Dinkin Duniya UNESCO, ta saka yankin cikin wuraren tarihi na duniya a 2002.
Hanyar Kogin Moselle
Tafiya a gabar Kogin Moselle da jirgin kasa a Jamus, tafiya abin birgewa. Za ka dau hanya daga birnin Koblenz inda Kogin Rhine da na Moselle suka hadu. A na wuce kauyuka da tsaunuka abin sha'awa da dama kamar Cochem an der Mosel. Kamfanin jirgin kasan Jamus na bin hanyar Moselle daga Koblenz zuwa Trier. Farashin mai sauki, zai ba da damar ya da zango a hanya kafin ci gaba da bulaguro.
Lindau a gabar ruwan Constance
Jiragen kasan da ke bin hanyar gabar ruwan Constance a kudancin Jamus, sun fito da sabon tsari mai birgewa. Jirgin kasa samfurin RE5 ga misali, zai tashi daga Stuttgart ya kuma isa garin Lindau da ke Bavaria. Za a kwashe tsawon kilomitoci ana tafiya cikin daji mai dauke da fulawowi da koramu masu birgewa, kafin isa tsohon birnin da ke Tsibirin Lindau.
Munich zuwa Salzburg
A sauran birane kamar Berlin, za a iya sayen tikitin zuwa Munich a kan kudi Euro tara a watannin Yuni da Yuli da kuma Agusta. Sai dai a yanzu matafiya na iya daukar jirgin kasa da zai zagaya daukacin yankin har zuwa birnin Salzburg na Ostiriya, inda za su bi ta Bavaria duk cikin wannan tikiti mai araha.
Hamburg zuwa Sylt
Tsawon kwanaki 90, zai fi sauki fiye da kowanne lokaci zuwa Tsibirin Frisian da ke gabar teku. Daga birnin Altona na Hamburg, mutum zai iya daukar jirgin kasa samfurin RE6 kai tsaye zuwa tsibirin da ke gabar teku wanda kuma ke karbar bakuncin dimbin masu yawon shakatawa. Bulaguro zuwa tsibirin, na daukar tsawon sa'o'i hudu kacal.
Dresden zuwa Decin a Jamhuriyyar Chek
Yawatawa cikin garin Saxon Switzerland a Jamus dauke da duwatsu abin birgewa, na da matukar dadi a jirgin kasa. Za a bi ta Kogin Elbe daga birnin Dresden zuwa Bad Schandau, inda masu hawan dutse da dama ke farawa. Za kuma a iya karasawa garin Decin da ke Jamhuriyyar Chek, wanda hakan zai ba yar da damar ganin wajen shakatawa daga bangaren Chek din wato Bohemian Switzerland.
Daga Gera zuwa Cheb ta hanyar Göltzschtal Viaduct
Masu sha'awar yin tafiye-tafiye a jirgin kasa, za su samu damar bi ta kan gadar da aka gina da bulo mafi girma a duniya wato Göltzsch Viaduct da jirgin kasa samfurin RB4 da RB2. Za a bi ta gabar ruwan Elster daga Gera zuwa Cheb a Jamhuriyyar Chek. Ka da ku manta, wannan tikiti mai araha bai shafi tafiya a jiragen kasa samfurin ICE da IC da EC da kuma Flixtrain ba.
Munich zuwa gabar ruwan Tegernsee
Guri mai matukar birgewa a Jamus, kewaye da tsaunuka. Za a iya zuwa wurin yawon bude idanu na gabar ruwan Tegernsee da tikitin mai araha a tsawon kwanaki 90 na lokacin hutun bazara. Daga birnin Munich, mutum zai iya daukar jirgin kasa samfurin Bavarian Overland zuwa garuruwan da ke gabar ruwan mai birgewa: Gmund a can karshen arewaci da kuma Tegernsee gari na karshe.
Berlin zuwa Tekun Baltic
Hutun bazara ba zai kammala ba a Berlin ba tare da tafiya zuwa gabar Tekun Baltic ba. Godiya ga tikiti mai rahusa, za a samu saukin zuwa garuruwa kamar Stralsund (cikin hoton), da jiragen kasa. Sai dai kamfanin jiragen kasa na Deutsche Bahn, ya yi gargadin cewa ba a yadda mutum ya shiga da keke jirgin da za a samu cunkuso cikinsa a watan Agusta ba, sai dai ya yi hayar keken a inda zai je.