1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Za´a gudanar da taro don daukar mataki daya kan Iran

April 29, 2006
https://p.dw.com/p/Bv0G

Sakatariyar harkokin wajen Amirka Condoleezza Rice ta kira wani taron membobi 5 masu kujerun dindindin a kwamitin sulhu na MDD hade da Jamus don tattunawa akan wani mataki na bai daya da za´a dauka kan Iran dangane da aiwatar da shirinta na nukiliya. Rice ta yi wannan kira ne bayan da hukumar MDD dake sa ido a ayyukan nukiliya wato IAEA ta gabatara da wani rahoto wanda ya samu Iran da bijirewa kiran da MDD ta yi na ta dakatar da shirin inganta uranium. A ranar 9 ga watan mayu za´a gudanar da taron na ministocin harkokin wajen kasashen guda 6. A kuma can birnin New York jami´an diplomasiya kasashen yamma suna shirin gabatarwa kwamitin sulhu wani kuduri a tsakiyar mako mai zuwa wanda zai bukaci Iran ta yi watsi da shirin na nukiliya.