1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Za´a gudanar da zabe yadda aka tsara a Pakistan..

Ibrahim SaniNovember 8, 2007
https://p.dw.com/p/C5b9

Shugaba Pavez Musharraf na Pakistan ya ce shirye –shirye sunyi nisa na gudanar da zabe a kasar,a ranar 15 ga watan fabarairun sabuwar shekara. Da alama dai ɗaukar wannan maki nada nasaba ne da kiraye kirayen da ake na lallai ya gudanar da zaben, yadda aka tsara ne tun da farkon fari. Kafafen yada labarai sun rawaito ministan yada labarai na kasar na Jaddada bayanin na Mr Musharraf:

Mr Tariq Azim Khan ya ce Mr Musharraf zai ajiye shugabancin sojin kasar da zarar ya yi ta zarce a karo na biyu, batun zaɓe kuwa abune da aka shirya gudanar dashi a ranar 15 ga watan Janairun sabuwar shekara,a don haka ƙorafin da ´Yan adawa suke bashi da tushe.

Har ilya yau shugaban na Pakistan ya kuma tabbatar da cewa nan da wata ɗaya ko biyu, zai cire dokar ta ɓaci daya kafa a kasar.Gwamnatin ta Pakistan dai na ci gaba da tsare ´Yan adawa na kasar, waɗanda suka shiga zanga zangar bore da matakin na Mr Musharraf. A gobe ne dai shugabar adawa ta ƙasar, Benazir Bhutto ta ce zata jagoranci wani gangami na adawa da matakan na shugaba Musharraf.´Yan adawa na kasar na sukan shugaban ne da karan tsaye ga dokoki na kasa,wanda hakan ya haifar da saka dokar ta ɓaci.