1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zabe a kasar Iran

March 2, 2012

'Yan takara fiye da dubu uku na fafatawa a zaben 'yan majalisar dokokin Iran

https://p.dw.com/p/14DJh
An Iranian woman casts her ballot for parliamentary elections at a polling station in Tehran, Iran, Friday, March 2, 2012. Nearly 47,000 polling stations throughout Iran take ballots for Iran's 290-member parliament, a vote seen as a political battleground for competing conservative factions in the absence of major reformist parties, which were kicked out of power over the 2009 post-election riots. More than 48 million Iranians are eligible to vote. (Foto:Vahid Salemi/AP/dapd)
Hoto: dapd

A na ci gaba da zaben 'yan majalisar dokoki a kasar Iran.
A jimilce 'yan takara 3.400 ne su ke fafatawa domin zama a Majalisar kasar mai kujeru kusan 300.
Ofishin ministan cikin gida dake kula da shirya zaben ya ce mutane fiye a miliyan 48 ne ta kamata suka kada kuri'a.Rukunin jam'iyun masu ra'ayin rikau suna kalubalantar masu goyan bayan shugaban kasa Mahamud Ahmadinedjad da suke zargi da nakasa tattalin arzikin kasa, da kuma nuna sassaucin ra'ayi game da addini.
A daya wajen,akwai jerin 'yan takara masu akidar neman sauyi, to saidai kiddidigar jin ra'ayin jama'a ta hango cewa ba za su kai labarai ba.
Wannan zabe wanda shine nan farko tun bayan zaben shugaban kasa a shekara 2009,na matsayin zakaran gwajin dafi ga shugaba Mahamud Ahmadinejdad da 'yan adawa ke zargi da assasa cin hanci da rashawa da kuma take hakkokin jama'a.

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Usman Shehu Usman