Zaben Aljeriya cikin halin rashin jin dadi
May 9, 2012Gwamnatin Aljeriya ta sanar da cewar zaben kasar da zai gudana ranar Alhamis, zai kasance mafi inganci a tarihin kasar, saboda haka ma ta gaiyaci masu sanya idanu na kasa da kasa. Shugaba Abdelaziz Bouteflika ya kwatanta zaben a matsayin wata sabuwar dama ga matasa. To sai dai duk da haka, babu wata sha'awa mai karfi tattare da wannan zabe. Al'ummar Aljeriya suna matukar fushi saboda tsadar kayan masarufi fiye da kima da cin rashawa da kuma rashin aiwatar da gyare-gyare cikin gagawa. Rashin yarda da al'ummar Algeria suke nunawa shugabanninsu na siyasa, ya sanya jam'iyu masu akidar musulunci suke baiyana fatan samun karin goyon baya a zaben na gobe.
Aisha tace ta kasa fahimtar yadda farashin kaya suka yi tsada a kasar a Aljeriya, mussamman masarufi na yau da kullum, kamar kayan marmari ko dankalin turawa da ya zama babban abincin al'ummar kasar.
Tace mu kam mun gaji. A duk lokacin da muka shiga kasuwa, mukan ga abubuwa masu tari yawa da muke so, amma bama iya sayen su, saboda komai yayi tsada. Ta yaya mutum zai iya ciyar da iyalinsa.
Wanna ma dai ita ce tambayar da Ali, wani mai sayar da kayan marmari a birnin Bab el Oued yayi, saboda masu ciniki dashi kullum sai raguwa suke yi. Ali yace kafin zaben, yan siyasa da yawa sanye da kaya masu tsada sun zo nan, kuma gaba dayan su, sun yi ta kampe na neman kuri'unmu. To sai dai ni bani da sauran wani abin yi da siyasa, kamar dai mafi yawan mu a Bab el Oued.
Babu wanda zai je kada kuri'ar sa a nan. Matasa a wannan wuri aikin yi suke so, to amma gwmnati bata yi masu komai, yan siyasa basa komai sai yi mana alkawuran da basa cikawa. Ina da takardar shaidar babbar makaranta, har ma na koyi aikin lauya, amma duk da haka gani ina zaune a nan, bani da komai. Da yawa daga ciki mu sun janye zuwa Turai, amma wasu cikin mu sun gwammace su ci gaba da zama a nan, kamar yadda akan ce wai bakin da Allah ya tsaga, baya hana shi abinci.
A Aljeriya dai babu wani abin da ya canza. Yan kasar suna rayuwar su ne cikin halin bakin ciki da rashin jin dadi. A ta bakin hukuma, kashi 20 cikin dari ne na yan Aljeriya basu da aikin yi, inda matasa basa hangen wani haske ga makomar su, musamman a kasa kamar Algeria, inda mafi yawan mazauna kasar basu ma kai shekaru 30 da haihuwa ba. Matasa sukan ce wai sun daina sa ran zasu sami wani abin kirki daga wannan zuriya ta kakannin su da suka mulki kasar tsawon shekaru 50... Le Pouvoir, wato karfin iko, abu ne da a Aljeriya yanzu yake hannun wani rukuni na yan siyasa da janarori da jami'an gwamnati da basa komai sai cin rashawa. Sune masu mallakar arzki da dukiyar kasar, wato man fetur da gas, yayin da mafi yawan talakawan kasar basa samun komai daga wannan dukiya. Saboda haka bai zama abin mamaki ba ganin cewar kusan ace babu wanda yake nuna sha'awar sa ga jam'iyu arba'in da zasu shiga zaben majalisar dokokin, musamman ganin cewar ita kanta majalisar bata wuce yar amshin shatan masu mulkin ba. Masanin rayuwar dan Adam, Nacer Djabi yake cewa:
Wannan dai ita ce matsalar. Matasa suna kira ga samun canji, amma wadanda ya kamata su aiwatar da canjin sun ki aiwatar dashi ta fuskar siyasa. Bamu da yan siyasar dake son kawo canjin. Saboda haka ne ma ko wace irin zanga-zanga takan zama bata da amfani, abin dake sanyawa mutane rika zuwa kan tituna suna kunnawa kansu wuta su kone kansu saboda adawa. Duk wannan baya kawo canji, saboda babu wanda zai iya tsara yadda za'a sami canjin. Aljeriya ta zama kasar da matsaloli suka dabaibaye ta, amma babu mai iya kawo yadda za'a shawo kan wadannan matsaloli.
Jam'iyun kasar masu akidar musulunci dake da sassaucin ra'ayi, suna kokarin amfani da wannan hali da Aljeriya take ciki domin cin ribar su. Duk da haka, jam'iyar FLN ta shugaban kasa Abdelaziz Boutelfika ta zura ido ta ga irin rawar da jam'iyun na musulmi zasu taka a zaben, koda shike tayi imanin a karshe dai ita ce zata sami nasara, tare da goyon bayan masu kada kuri'u.
Mawallafi: Alexander Göbel/Umaru Aliyu
Edita: Halima Balaraba Abbas