1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaben Aljeriya na cikin rudani

March 22, 2014

Dubban masu goyon bayan 'yan adawa sun yi zanga-zangar fatali da sake tsayuwa takara na Shugaban Aljeriya Abdelaziz Bouteflika a zaben mai zuwa

https://p.dw.com/p/1BUDc
Hoto: FAROUK BATICHE/AFP/Getty Images

Dubban magoya bayan 'yan adawa na kasar Aljeriya sun gudanar da gangami na nuna rashin amincewa da Shugaba Abdelaziz Bouteflika ya sake takaran shugabancin kasar karo na hudu, bayan ya shafe shekaru 15 kan madafun ikon kasar da ke yankin arewacin nahiyar Afirka.

Masu gangamin sun nemi kaurace wa zaben idan har Bouteflika dan shekaru 77 da haihuwa, ya sake tsayawa takara yayin zaben na ranar 17 ga watan gobe na Afrilu.

Shugaban kasar ta Aljeriya Abdelaziz Bouteflika yana fama da rashin lafiya, amma saboda yadda jam'iyya mai mulki ta mamaye komai na kasar ake gani babu makawa zai sake samun nasara.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Pinado Abdu Waba