1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka: Corona da zaben shugaban kasa

Ines Pohl ATB/LMJ
July 31, 2020

Mai yiwuwa kasar Amirka, ba za ta farfado daga annobar COVID-19 da ta nakasa tattalin arzikinta kafin zaben da ake shirin gudanarwa a watan Nuwambar bana ba.

https://p.dw.com/p/3gEAW
USA Präsident Trump
Shugaban Amirka Donald TrumpHoto: Reuters/L. Millis

A sharhinta da ta rubuta, babbar Editar tashar DW Ines Pohl na ganin wannan tunanin na Trump na da matukar hadari. Ines Pohl din dai ta ce shugaban Amirka Donald Trump ya yi dukkan bakin iyawarsa don kin yarda da cewa annobar COVID-19 na da hadari. Ya sha yin karerayi da ki fadi da yada bayanai masu rikitarwa domin kawar da hankulan jama'a, inda a baya-bayan nan ya kambama da'awar wani likita wanda yace za a iya magance corona ta amfani da wasu kwayoyin hallita na DNA.

Matsin tattalin arziki mafi muni

Trump dai ya zabi ya kare tattalin arzikin kasa fiye da lafiyar al'umma, abin da ke zaman babbar kasada. Sakamakon da aka gani kuwa, shi ne karuwar mace-mace, wanda ya zuwa yanzu yawan wadanda corona ta lakume rayukansu ya kai kimanin mutane dubu150, baya ga koma bayan tattalin arziki mafi muni da aka gani a tsawon tarihi. Babu dai wani haske na kawo karshen wannan labari, mace-mace na dada karuwa kamar yadda Amirkawa ke ci gaba da zama cikin zullumi da fargaba na yiwuwar kamuwa da cutar. Wannan ko shakka babu, ba abu ne mai dadi ba ga ci-gaban kasuwanci da tattalin arziki.

Ines Pohl Kommentarbild App
Ines Pohl shugabar ofishin DW na birnin WashingtonHoto: DW/P. Böll

Ines Pohl ta ce tattalin arzikin duniya na fuskantar mawuyacin haliz, yayin da haske na yiwuwar sake zabar Trump ke kara dusashewa, kuma idan tattalin arzikin ya ci gaba a haka, to kuwa labudda wannan shugaban mai yawan alkawura, ba zai iya cin zaben na ranar uku ga watan Nuwamba ba. Wani abin la'akari shi ne yayin da gazawar Trump ke kara baiyana, haka ma dukkan yunkurinsa ke kasancewa. Alal misali. jim kadan bayan da a ranar Alhamis aka sanar da alkaluman kididdiga cewa abin da Amirka ke samu a shekara ya ragu da kimanin kaso 30 cikin dari a zango na biyu na wannan shekarar, Trump ya fito da shawarar dage zabe, wanda ya wallafa a shafinsa na Twitter.

Sannan ya kara nanata cewa yin zabe ta hanyar aikewa da kuri'a ta gidan waya zai haifar da magudi, duk da cewa bai bayar da wata hujja da za ta tabbatar da zargin ba. Bai damu ba kuma ko a jikinsa, ballantana ya ji ko akwai wata madogara ta shari'a da za ta sanya dage zaben saboda annobar corona.

USA Portland | Black Lives Matter | Protest gegen Rassismus
Me yasa Trump ya tura sojoji PortlandHoto: Imago Images/ZUMA Wire/M. KcKenna

A bayyane ta ke dai cewa yayin da zaben ke karatowa, Trump na shirin ya jefa Amirka cikin wani rudani da kassara tushen dimukuradiyyarta. Wannan shi ne manufar take-takensa na siyasa a baya-bayan nan. Abin tambaya ma shi ne, mai ya sa ya tura jami'an tsaro na tarayya zuwa Portland? Tabbas ba domin su kwantar da tarzoma ba ne, sai don su assasa rikici da raba kawunan jama'ar kasar.

Makomar Trump da Republicans

Joe Biden da wasu yan Democrats irinsu Bernie Sanders tuni suka yi kashedin cewa Trump ba zai bar mulki ba tare da turjiya ba. Yayin da alamu ke nuna yiwuwar ya sha kaye, haka zarginsu yake kara tabbata. Ines ta kammala da cewa gaskiyar lamari, inda 'yan jam'iyyarsa ta Republicans da dama ke nesanta kansu daga gare shi. Watakila alama ce ta alheri. Sun fara fahimtar cewa ba za su sami wata makoma ta gari ba idan suka ci gaba da goya masa baya, kuma a karshe suma laifin zai shafe su.