Zaben Amirka: Nasara da shan kaye
Bei den Kongresswahlen in den USA geht es nicht nur um Politpromis. Schlagzeilen machen auch Native Americans, Muslimas und Homosexuelle. Ein Überblick über außergewöhnliche Gewinner und Verlierer.
'Yar gudun hijira, Musulma, 'yar majalisa
'Yar jam'iyyar Democrats Ilhan Omar ta zama Musulma ta biyu da ta samu kujera a majalisar dokokin Amirka. 'Yar asalin Somaliya mai shekaru 37 da haihuwa ta tsaya takara a jihar Minnesota. Iyayenta sun guji yakin basasa lokacin da take da shekaru takwas a duniya.
'Yar siyasa da ke da tushe da Falasdinu
Rashida Tlaib na daya daga cikin Musulmi biyu da suka zama 'yan majalisan dokokin Amirka. Bayan da ta samu kashi 88 cikin 100 na kuri'un da aka kada, 'yar asalin Falasdinu mai shekaru 42 da haihuwa ta lashe mazabar Michigan. Amma nasararta ta bayyana tun kafin zaben saboda babu dan takarar Republicans a Michigan.
An samu 'yar asalin Amirka a majalisa
'Yar jam'iyyar Democrats Deb Haaland ta zama 'yar asalin Amirka na farko da aka zaba 'yar majalisar dokoki. Ita lauyar mai shekaru 57 na sahun wadanda suka fito daga tsatson Amirka da suka tsaya takara kuma suka lashe zabe. A jihar New Mexico ta yi nasarar doke Janice Arnold-Jones ta jam'iyyar Republicans.
'Yar majalisa mafi karancin shekaru
Ita ce 'yar majalisar wakilai mafi karancin shekaru a tarihin Amirka: Alexandria Ocasio-Cortez mai shekaru 29 da aka zaba karkashin jam'iyyar Democrats. Ta samu nasara a New York inda mata da dama suka samu nasara: Akalla mata 28 ne suka samu kujera a majalisun kasar, lamarin da ya sa su shiga cikin tarihi.
Farkon gwamna dan luwadi
Dan Democrats Jared Polis ya kafa tarihi a Amirka: Ya samu rinjaye a jihar Colorado a kan dan takara na Republican Walker Stapleton a zaben gwamna. Polis ya zama gwamna na farko da ya bayyana a fili cewa shi dan luwadi ne.
Republicans da ke adawa da Trump
Mitt Romney ya kalubalanci Barack Obama a zaben shugaban kasar Amirka a shekara ta 2012, amma bai samu damar shiga fadar mulki ta White House ba. Sai dai mai shekaru 71 da haihuwa ya lashe kujerar majalisar dattawa a jihar Utah. Shi dan Republican din ya kasance mai sukar kamun ludayin Shugaba Donald Trump.
Tsohuwar kurar siyasar Amirka
Bai samu nasara a zaben fidda gwani na zaben shugaban kasa da ya gudana shekaru biyun da suka wuce ba, amma Bernie Sanders ya kare kujerarsa a majalisar dattawan Amirka. Tsohon dan siyasa mai 77 ya sake samun nasara a Vermont. Yana yunkurin tsayawa takara a 2016 a karkashin jam'iyyar Democrats . Ya zama abin kiyo ga masu matsakaicin ra'ayin gurguzu da ke neman jagora.
Sha-lelen Democrats ya sha kaye
An fuskanci hamayya mai tsanani a yunkurin lashe kujerar majalisar dattawa da ke wakiltar Texas, duk da cewa 'yan Republicans na da karfi a jihar: Dan Demokrat Beto O‘Rourke ( a hoto) ya sha kaye a hannun dan Republican Ted Cruz. Amma masharhanta sun yi imanin cewa Amirka za ta ci gaba da begen O’Rourke: Wasu na kwatanta shi a matsayin sabon Barack Obama.
Bakar fata gwamna? Ba yanzu ba
'Yar Democrats Stacey Abrams ta so zama bakar fata ta farko da ta rike mukamin gwamna a tarihin Amirka. Ta ma kasance mace mai tsatson Afirka ta farko da manyan jam'iyyun kasar biyu Democrats da Republican suka taba tsayarwa takara. Sai dai ta gaza kai labari: Ta sha kaye a Georgia a gaban dan Republican Brian Kemp.
Gudunmawar Obama bai taimaki Gillum ba
Shi ma dan Democrats Andrew Gillum ya so zama dan asalin Afirka na farko da zai dare kan kujerar gwamna a jihar Florida. Amma ya kasa kai labari a gaban dan takarar Republicans Ron DeSantis. Tsohon shugaban Amirka Barack Obama ya taimaka wa Gillum gudanar da yakin neman zabe.
Babu nasara ga gwamna mata-maza
'Yar Democrats Christine Hallquist ta so zama gwamna ta farko mata-maza a tarihin Amirka. Amma Hallquist ta sha kaye a Vermont a gaban dan takarar Republican Phil Scott, wanda ya lashe kashi 55 cikin 100 na kuri'un da aka kada - duk da cewa jihar ta kunshi dimbin masu ra'ayin ci gaba.