Shugabanin kasashen duniya na taya Joe Biden murna
November 9, 2020Zababben Shugaban Amirka Joe Biden na ci gaba da karbar sakonnin taya murna daga ciki da wajen nahiyar Amirka. Daga bangaren kudu da arewa gabas da yamma ko ina ka juya a wannan duniya, jama'a na mayar da martani, galibi ana murnar lashe zaben wanda Shugaba Trump ke ci gaba da kartar kasa kan sakamakonsa. Kungiyar Tarayyar Turai ta EU na cikin wadanda suka ce a shirye suke su yi aiki tare da zababben Shugaba Joe Biden.
Aika sakonnin murna daga sassan duniya
Shugabar hukumar gudanarwa ta kungiyar Ursula von der Leyen ta bayar da tabbaci tana mai cewa..''Ina son tabbatar muku da cewa Kungiyar EU a shirye take ta kara fadada hadin gwiwarta da sabon shugabancin na Amirka. Akwai gagarumin aiki a gabanmu amma za mu iya dorawa daga dangantarkar da muke da ita da su a halin yanzu.''To sai dai ga Firaminsitan Birtaniya Boris Johnson batun kasuwanci da sauyin yanayi, su ne zai so zababben shugaban na Amirka ya mayar da hankalinsa a kai..''Ina fatan yin aiki kafa da kafa da shi, kan abubuwa masu muhimamnci a nan gaba kadan. Ina son mu duba batun magance sauyin yanayi da kasuwanci da kuma samar da tsaro a kasashen duniya.''
Bude sabon babi tare da Joe Biden
Birtaniyar da Jamus da Faransa na cikin sahun farko na kasashen da suka taya zababben shugaban Amirkan murna, inda tun ma a karshen mako Ministan Harkokin Wajen Jamus Heiko Maás ya soki tirjiyar da Shugaba Trump ke yi kan sakamakon zaben, inda Maas ya ce mutanen da suka fadi zabe kuma suka rungumi kaddara sun fi mutanen da suka yi nasara a zabe taimaka wa dimukuradiyya. Wasu 'yan kasashen China da Iran da Japan da DW ta tattauna da su, dukkansu na ganin cewa Shugaban Amrka mai barin gado Donald Trump bai riki dangantar da ke a tsakanin Amirka da kasashensu da hannu biyu ba. Sai dai masu sharhi na cewa ga irin wadanann kasashe, Joe Biden ka iya bude musu sabon babi.