1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana ci gaba da kada kuri’a a zaben shugaban kasa

Gazali Abdou Tasawa AMA
February 21, 2021

A Jamhuriyar Nijar al’umma na ci gaba da kada kuri’a a zaben shugaban kasa zagaye na biyu don tantance wanda zai jagoranci kasar na tsawon shekaru biyar masu zuwa.

https://p.dw.com/p/3pfNu
Niger | Präsidentschaftswahlen in Zinder
Hoto: Mohamed Tidjani Hassane/DW

Da misalin karfe takwas na safe ne akasarin rumfunan zabe suka bude a birnin Yamai, rumfar zabe mai lamba 001 inda shugaban kasa da sauran mambobin gwamnati da manyan jami’an gwamnati da 'yan siyasa ke kada kuri’ar tasu. Bayan kada kuri’arsa, shugaban kasa Alhaji Mahamadou Issoufou ya bayyana gamsuwarsa da wannan rana wacce ya bayyana a matsayin ta tarihi yana mai cewa "Ina mai farin cikin kasancewa zababben shugaban kasa na farko a tarihin kasar nan da ke shirin mika mulki ga wani zababben shugaban kasa, abun alfahari ne ga siyasar kasar nan."

Niger | Präsidentschaftswahlen in Zinder | Kandidat Mahamane Ousmane
Mahamane Ousmane dan takarar shugaban NijarHoto: Mohamed Tidjani Hassane/DW

Dan takarar jam’iyyar adawa Alhaji Mahamane Ousmane ya gudanar da nashi zabe ne a mahaifarsa ta Damagaram, a yayin da dan takarar jam’iyya mai mulki Malam Bazoum Mohamed wanda shi ma dan jihar ta Damagaram ne ya gudanar da na shi zabe a birnin Yamai. Jama’a dai na yanzu ci gaba da yin tururuwa zuwa runfunan zabe domin kada kuri’ar tasu a birnin Yamai da sauran yankunan kasar duk da jinkirin da aka samu a wasu sassan Nijar na rashin bude rumfunan zabe da wuri.

Hukumar zaben kasar ta Nijar ta ce kawo yanzu babu wata matsala a cikin tafiyar da zaben, sai dai ta ce ta bankado wata manakisa ta neman shirya magudi. Ya zuwa yanzu dai zaben na gudana a cikin tsanaki a cikin birnin na Yamai inda aka jibge tarin jami’an tsaro a bakin rumfunan zabe da a wasu manyan titunan birnin Yamai don ganin zaben ya wakana a cikin kwanciyar hankali da lumana.